7 Yuni 2026 - 08:13
Source: ABNA24
Bahrain Ta Haramtawa ‘Yan Shi’ar Kasar Tafiya Zuwa Iran Da Iraki Tare Da Kwace Dukiyoyinsu

Gwamnatin Al Khalifa a Bahrain ta ƙara tsananta zalunci akan 'yan Shi'a a ƙasar, inda ta haramta musu tafiya zuwa Iran da Iraki, tana mai kwace waqafin dukiyar mabiya mazhabar Ja'fari, kuma tana kame malaman addini da shugabannin 'yan Shi'a.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya bayar da rahoton cewa: Wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da Amurka ke yaƙi da Iran, kuma maimakon gwamnatin Bahrain ta haɗa kai da jama'arta don fuskantar rikicin waje, sai ta mayar da hankalinta kan danniya da tsananta wa 'yan Shi'a, tana mai ɗaukar su a matsayin maƙiya maimakon tushen tsaron ƙasa.

Wani mai fafutuka Dr. Rashid Al-Rashed ya bayyana cewa wadannan matakan ba na tsaro ba ne, sai dai na siyasa ne don ɓoye gazawarsu a yaƙi da Iran. Hakan yana nuna cewa gwamnatin Al Khalifa ta fi damuwa da 'yan Shi'ar Bahrain fiye da kare ƙasar daga hare-haren waje.

A ƙarshe, wannan zaluncin da gwamnatin ke yi bai iya ɓoye wulakancin da gwamnatin ta sha a hannun 'yan Shi'a da kawancenta ga kasashen waje a duniya ba.

……………………..

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha